An sace matan Aure 3 a kauyen dorayi

A ranar Asabar da ta gabata ne wadansu mutane dauke da miyagun makamai suka kewaye wata rugar Fulani da ke kauyen dorayi a gundumar Dutsen Abba ta karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna inda suka sace Fulani matan aure uku.Maharan su kusan 50 dauke da bindigogi sun isa rugar ce da misalin karfe 9:00 na […]

An sace matan Aure 3 a kauyen dorayi
An sace matan Aure 3 a kauyen dorayi

A ranar Asabar da ta gabata ne wadansu mutane dauke da miyagun makamai suka kewaye wata rugar Fulani da ke kauyen dorayi a gundumar Dutsen Abba ta karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna inda suka sace Fulani matan aure uku.
Maharan su kusan 50 dauke da bindigogi sun isa rugar ce da misalin karfe 9:00 na dare inda bayan awon gaba da matan 3 suka sace babur da shanu biyu.
Aminiya ta ziyarci kauyen inda da wata gyatuma (an sakaya sunanta) ta ce, “Da misalin karfe 9:30 na dare mutanen kimanin hamsin dauke da bindigogi suka kewaye gidanmu suka shiga bi daki-daki suna fito da duk wanda ke ciki, daga baya suka tsame wadansu matan aure  uku da shekarunsu ba su kai 20 ba, wato Hauwa’u da Maimuna da Mairo da ba su wuce shekara biyu da aure ba, kuma ba wadda ta taba haihuwa suka tafi da su. Na yi ta ba su hakuri amma suka ki saurarena.”
daya daga cikin mazajen matan ya shaida wa wakilinmu cewa, “Ina cikin garke domin kula da shanu aka bugo mini waya cewa ga abin da ke faruwa, sai na yi ta kokarin sanar da makwabta domin su kawo mana dauki. Kowa sai ya ce sai dai mu taya ku da addu’a domin wadannan mutane ba su da imani kuma suna dauke da miyagun makamai, duk wanda suka yi arangama da shi kashe shi za su yi. Haka suka kwashe matan da shanu da babur suka kwace wayoyin mutanen gidan duka.”
Da Aminiya ta tuntubi Sarkin dorayi, Malam Lawal Ahmad, ya ce, “Ba mu taba ganin irin wannan tashin hankali ba, kuma bayan a cikin dare ranar Asabar sun tafi da matan 3, washegari sun sake dawowa suka dauke shanu da babur suka tafi. Yanzu haka mun dauki matakai, mun sanar da hukumomin, kuma za mu kara daukar matakan da suka dace na tsaro, kuma na kira taro domin karfafa hadin kanmu.” Ya ce daga baya maharan sun kira ta waya, sun ce matan suna nan lafiyarsu, sai dai ba su yi maganar kudin fansa ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Zubairu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sun dauki matakan da suka dace na kyautata tsaro a yankin da kuma binciken lamarin