An Sace Mutane 20 A Abuja

Mutum daya na samun kulawa a asibiti sakamakon raunin harbi a yayin musayar wuta

An Sace Mutane 20 A Abuja

’Yan sanda. (Hoto: NAN)

Wasu ’yan bindiga masu satar mutane sun kai hari unguwar Dawaki da ke Abuja, in da suka yi awon gaba da mutane 20.

Shugaban unguwar, Tunde Abdulrahim, ya ce ’yan bindigar da adadinsu ya kai 50, dauke da muggan makamai sun shiga rukunin gidaje na Dawaki Rock Heaven ne kafin Sallar Isha’i na yammacin ranar Lahadi.

Harin ya tashi hankalin jama’ar yankin, lura da cewa ’yan bindigar sun shiga gidaje har guda shida suna daukar mutane.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce jami’ansu karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda CP Benneth Igweh sun yi nasarar ceto duk wadanda aka sace.

Ta ce, “Mun samu kiran gaggawa daga unguwar Dawaki da misalin karfe 11:30 na daren ranar Lahadi, nan take Kwamishina, CP Benneth Igweh ya jagoranci runduna domin fuskantar ’yan bindigar”.

Josephine ta ce Kwamishinan da jami’ansa sun yi wa ’yan bindigar kofar rago a Ushafa da ke yankin Bwari, inda suka yi nasarar ceto mutanen da aka sace.

Kawo yanzu dai akwai mutum guda a asibiti yana karbar magani sakamakon rauni da ya samu sanadiyyar harbin bindiga.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume