An sace mutum uku ’yan gida daya a Katsina
A ranar Litinin da dare ’yan bindiga suka shiga gidan wani Malam Shamsudden Yusuf da ke Rukunin Gidajen Ma’aikatan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Dutsimma, inda suke yi garkuwa da matarsa Nana Bilkisu da kanwarta A’isha Salisu da ’yarsa Afnan Shamsu. Wata majiya ta ce masu garkuwar sun bukaci fansar Naira miliyan 20. Kakakin Rundunar ’Yan sandan […]
A ranar Litinin da dare ’yan bindiga suka shiga gidan wani Malam Shamsudden Yusuf da ke Rukunin Gidajen Ma’aikatan Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Dutsimma, inda suke yi garkuwa da matarsa Nana Bilkisu da kanwarta A’isha Salisu da ’yarsa Afnan Shamsu.
Wata majiya ta ce masu garkuwar sun bukaci fansar Naira miliyan 20. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin.
A wani labarin daban, an yi garkuwa da wani magidanci Sanusi Lawal, kanen Dagacin kauyen Dayi Malam Yahaya Lawa da matarsa a gidansa da ke Dayi a Karamar Hukumar Malumfashi. Masu garkuwar na neman Naira miliyan 6.