An sace N50bn daga asusun Gwamnatin Kano —Muhyi

An sace miliyan 450 da sunan sayen gidajen sauro masu ɗauke da magani

An sace N50bn daga asusun Gwamnatin Kano —Muhyi

Muhyi Magaji Rimin-Gado

Hukumar Yaki da Rashawa ta Jihar Kano ta bankaɗo badaƙalar satar kuɗi sama da Naira biliyan 50 a ƙananan hukumomi 44 da ake jihar.

Shuagaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce hukumar ta kuma gano wata badaƙalar Naira miliyan 450 da aka sace daga asusun jihar da sunan sayen gidajen sauro masu ɗauke da magani.

Ya shaida wa mahalarta wani taron ƙara wa juna sani cewar, “Mun gano Naira biliyan 50 da aka sace daga asusun jiha, kuma ,ina da shaidu kimanin 145.

“Sannann mun gano waso gidaje da otel-otel masu alaƙa da kuɗaɗen satan da  a biranen Dubai, London, da kuma Abuja.”

A cewarsa, da hukumar ta yi yunƙurin binciken wanda ake zargibda badakalar Naira miliyan 450 na gidajen sauro, amma ya garzaya kotu neman umarnin hana ta binciken shi.

Muhyi ya bayyana wa mahalarta taron, waɗanda jami’an hukumomin yaƙi da rashawa ne daga jihar da ma tarayya cewa, kashi 80% na satar kuɗin gwamanti da ak yi a Jiahr Kano, an yi ne da sunan sayen kayan gwamnati.

Ya ce hanyoyin sun haɗa da aringizon farashi, sayen kasa da abin da aka tsara, ko ma rashin yin sayayyar bayan an biya kuɗaɗen.

Da yake jawabi, wakilin daraktan Hukumar EFCC Shiyyar Kano a taron, CSP Aminu Bashir,  ya bayyana cewa kashi 95% na satar kuɗaɗen gwamnati ana yin su ne a wurin yin sayayya.

Don haka ya shawarci jami’an gwamnati da su rika bin ka’idodi da dokokin yin sayayyar gwamnati domin guje wa fushin shari’a ko shiga rikici.

A nasa ɓangaren, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya wakilta, ya bayyana cewa, satar kuɗaɗen gwamnati ba ta yiwuwa sai da haɗin bakin jami’an gwamnati.

Ya ce gwamnatin Abba ba za ta lamunci satar kuɗin gwamanti ko rashawa ba, domin a cewarsa, Jihar Kano ta ga mummunar illar satar kuɗin gwamanti a shekaru takwas da suka gabata, wanda a hakan ya hana wa jihar samun cigaba.