An sace Naira miliyan 500 a Hukumar Alhazai ta Jihar Bauchi
Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar Bauchi Alhaji Uba Ahmed Nana ya nuna damuwa kan yadda tsohuwar gwamnatin Malam Isa Yuguda ta sace Naira miliyan 500 a Hukumar Alhazai ta jihar a lokacin mulkinta. Alhaji Uba Nana ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Litinin, […]
Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar Bauchi Alhaji Uba Ahmed Nana ya nuna damuwa kan yadda tsohuwar gwamnatin Malam Isa Yuguda ta sace Naira miliyan 500 a Hukumar Alhazai ta jihar a lokacin mulkinta.
Alhaji Uba Nana ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Litinin, inda ya ce, tsohuwar gwamnatin ta kuma lalata komai kuma an kwashe motocin gwamnati masu dimbin yawa an bar sabuwar gwamnatin jihar da gadon bashin albashin ma’aikata na wata biyu.
Shugaban ya ce Gwamnan Jihar, Mohammed Abubakar ya sha alwashin zai yi iya bakin kokarinsa wajen farfado da martabar aikin gwamnati a jihar kuma ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa ba za su lamunci barin wasu ’yan tsirarun mutane sun rika facaka da dukiyar al’umma ba.
Sai ya shawarci al’ummar Jihar Bauchi su kwantar da hankalinsu domin sabuwar gwamnatin za ta toshe duk hanyoyin da ake sace kudin al’umma a gwamnatance.