An sace Naira tiriliyan 21 zuwa kasashen waje a shekara 10 – EFCC
Shugaban Hukumar Yaki da Tu’annati ga Tattalin Arziki ta kasa (EFCC) Malam Ibrahim Lamorde ya ce akalla Dala biliyan 129 (kimanin Naira tiriliyan 20 da biliyan 600) aka sace zuwa kasashen waje daga kasar nan cikin shekara 10 da suka gabata.Malam Ibrahim Lamorde ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata inda ya […]
Shugaban Hukumar Yaki da Tu’annati ga Tattalin Arziki ta kasa (EFCC) Malam Ibrahim Lamorde ya ce akalla Dala biliyan 129 (kimanin Naira tiriliyan 20 da biliyan 600) aka sace zuwa kasashen waje daga kasar nan cikin shekara 10 da suka gabata.
Malam Ibrahim Lamorde ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata inda ya ce Hukumar Tabbatar da Tsare Amanar Dukiya ta Duniya da ke Washington ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta bakwai a duniya wajen fitar da haramtattun kudade. Kuma hanyoyin samun kudaden sun hada da cin hanci da almundahana da kauce wa haraji da kin biyan haraji da hakar ma’adinai ta haramtacciyar hanya da kuma fataucin miyagun kwayoyi da na mutane.
Ya ce bangaren sanya ido kan mu’amala da kudi na Hukumar EFCC yya kiyasta cewa a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013, akala Dala biliyan 25 da miliyan 400, (kimanin Naira tiriliyan hudu da biliyan 64) aka fitar daga kasar nan ta hanyar daukar tsabar kudin a fita da su ta iyakokin kasar nan da kuma wasu cibiyoyin kudi.
Lamorde ya bayyana haka ne a wurin taron kara wa juna sani na yanki, kan inganta mu’amala da kudade da yadda ake kai-kawo da kudade a kan iyakokin kasashen Afirka ta Arewa da Afirka ta Yamma. kungiyar yaki da fitar da haramtattun kudade ta GIABA da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya ne suka shirya taron.
Malam Lamorde ya kara da cewa iyakokin mafi yawan kasashen Afirka shifcin gizo ne kawai, don haka ba su iya tagawa wajen hana kai da kawon kudade da ale samu a tsakaninsu, kuma masu aikata laifi na amfani da wannan dama.
Ya ce a kwanakin baya, “Wasu mutane sun shigo da dimbin takardun kudade cikin kasar nan a cikin motarsu. Sai aka gano su a kan iyaka kuma aka kama su.” Ya ce, abin mamaki sai wani gwamnan jihar da ke kusa da Najeriya ya rubuto wa takawaransa na Najeriya cewa a sake su, ’yan kasuwa ne ya san yadda suka samo kudin. Sannan wani sarki ya rubuto, “kuma jakadan kasar sau biyu yana ziyartata, inda na shawarce shi ya rubuta wa Ma’aikatar Harkokin Waje ya nemi sanya bakinta,” inji Lamorde.
A jawabin Jakadan kasar Swiss a Najeriya Hans- Rudolf Hodel ya ce taon bita ne kan irinsa da aka shirya bara domin duba irin kalubalen satar kudade zuwa kasashen waje. Ya ce taron zai mayar da hankali ne kan kalubalen fita da kudi ta barauniyar hanya da ba kungiyoyin ’yan ta’adda kudade.