An sace ragon layyan limami a daren Sallah a Filato

A daren Babban Sallah aka sace ragon layyan babban limamin unguwar Mista Ali da ke Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato

An sace ragon layyan limami a daren Sallah a Filato

Rago Balami

An sace ragon layyan Babban Limamin unguwar Mista Ali da ke Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato, Imam Abdulkadir.

An sace ragon liman Imam Abdulkadir ne a daren Babbar Sallah a lokacin da ake tsaka da ruwan sama a ranar Asabar.

Wani limami a unguwar, Malam Haruna Yaqub, ya bayyana haka ne a lokacin da yake huduba bayan kammala sallar idi, yana mai yin Allah-wadai da lamarin.

“A daren jiya aka sace ragon layyan da Babban Imam ya saya. Wannan abin mamaki da ban damuwa ne, domin ya nuna yanzu mutane ba su da tsoron Allah.

“Abin tsoro ne wannan tsabar rashin tsoron Allah da mutum zai je ya sace abin da aka tana domin aikin ibada,” in ji malam Yaqub.

Saboda haka Malam Yaqub ya ja hankali jama’a su kasance masu tsoron Allah su guji ayyukan laifi domin akwai ranar hisabi.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki