An sace tsohon Sakataren Gwamnati a Inugu
Maharan sun tazama mutane da harbi kafin sace tsohon sakataren gwamnatin
‘Yan Bindiga
’Yan bindiga sun sace tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Inugu, Dokta Dan Shere, tare da wasu matafiya da ba a tantace adadinsu ba.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Alhamis a hayar Enugu zuwa Ugwuogo, Nike zuwa Nsukka, a lokacin da Shere ke kan hanyarsa ta dawowa daga wani taro da ya halarta.
- Fargabar Hari: Sufeton ’Yan Sanda Ya Ba da Lambobin Kiran Gaggawa
- EFCC ta sake gurfanar da dakataccen Akanta Janar
Majiyarmu ta ce ’yan bindigar wanda adadinsu ya kai takwas, sai da suka yi harbe-harben bindiga a iska don razana jama’a kafin daga bisani suka yi garkuwa da su.
Sace mutanen ya jefa jama’ar yankin cikin mummunan tashin hankali, inda suka yi kira ga jami’an tsaro da a gaggauta daukar matakin ceto su.
Shere ya yi Sakataren Gwmanatin jiahr ne a zamanin tsohon Gwamnan Inugu, Chimaroke Nnamani.