An sace tsohon shugaban Jam’iyyar AC na Jihar Kaduna
A ranar Lahadin da ta gabata ne da misalin karfe 7:30 na dare wasu wadanda ake zato masu satar mutane su yi garkuwa da su ne suka sace tsohon shugaban tsohuwar Jam’iyyar AC ta Jihar Kaduna, kuma tsohon Ma’ajin Jam’iyyar PDP na jihar Alhaji Aliyu Yahaya Sa’ad.Aminiya ta ziyarci gidan dan siyasar mai shekara 68 […]
A ranar Lahadin da ta gabata ne da misalin karfe 7:30 na dare wasu wadanda ake zato masu satar mutane su yi garkuwa da su ne suka sace tsohon shugaban tsohuwar Jam’iyyar AC ta Jihar Kaduna, kuma tsohon Ma’ajin Jam’iyyar PDP na jihar Alhaji Aliyu Yahaya Sa’ad.
Aminiya ta ziyarci gidan dan siyasar mai shekara 68 da ke Layin Manchester a Unguwar Turawa (GRA) na Zariya, a inda ta tarar da cincirindon jama’a da suka je domin jajanta wa iyalansa. kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin mukasantar wanda aka sace ya ci tura, daya daga cikin kannensa mai suna Alhaji Abdullahi ya ce babban yayansu ya hana su ba da wani bayani a kan abin da ya faru, sai shi kadai ne zai mata bayani.
Da wakilinmu ya kiran lambarsa ta yi ta bugawa bai dauka ba, sai dai wani da bai son a ambaci sunansa a gidan ya ce, kamar yadda suka samu labari ya tafi Kaduna ta’aziya ne gidan marigayi Aliyu Jama’a tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya a kan hanyarsa ta dawowa sai ya biya gonarsa da ke Dumbun Dutse a hanyar Kaduna.Ya ce bayan ya yi Sallar Magriba a gonar ya fito domin dawowa shi da yaransa hudu a mota Pirado Jeep, sai wasu mutum uku a kan babur Bajaj suka zo kamar za su goga musu, sai mai gidan ya ce su kauce don kada su buge su, suka matsa har suka sha gabansu sai suka tsaya suka fito da bindigogi suka ce masu ina Yahaya Sa’ad. “To akwai wani suna da ake kiransa tun yana yaro A-yi-ta, sai daya da fuskarsa ke rufe ya ce ai ga A-yi-tan nan sai suka sauke wadanda suke motar sai suka kwantar da su suka kwace wayoyinsu suka tafi da shi a motar shi kuma mai tuka babur din ya bisu suka bar yaran a kwance,” inji majiyar, inda ya ce daga baya an samu motarsa a kauyen Amana da ke hanyar Jos.
Ya ce, ba su tunanin komai illa sun bar wa Allah tunda duk wasu harkokinsa bai cika yinsu ba illa harkar gona da kuma taba siyasa da ba a rasa ba. Ya ce, har zuwa lokacin babu wanda ya ce musu komai.
Da wakilinmu ya tuntubi Kwamnadan Yanki na ’Yan sanda ta waya sai ya ce ya tuntubi hedkwatarsu da ke Kaduna. Kakakin ’Yan sandan Jihar Kaduna SP Aminu Lawan ya tabbatar da aukuwar lamarin.