An sace tsohuwar ’yar Majalisar Jihar Nasarawa

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace tsohuwar ’yar majalisar Jihar Nasarawa daga Akwanga ta Kudu kuma tsohuwar shugabar marasa rinjaye a majalisar, Misis Mary Enwongulu a gidanta da ke Akwanga.  Wani makwabcin wadda aka sacen da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa “Lamarin […]

An sace tsohuwar ’yar Majalisar Jihar Nasarawa
An sace tsohuwar ’yar Majalisar Jihar Nasarawa

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace tsohuwar ’yar majalisar Jihar Nasarawa daga Akwanga ta Kudu kuma tsohuwar shugabar marasa rinjaye a majalisar, Misis Mary Enwongulu a gidanta da ke Akwanga. 

Wani makwabcin wadda aka sacen da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa “Lamarin ya auku ne da misalin karfe 1:00 na dare inda kafin ’yan bindiga da suka zo da yawa su sace tsohuwar ’yar majalisar, sun yi ta harbe-harbe na kusan awadaya.
Ya ce duk da sun kasa barci babu wanda ya fita daga bisani suka tafi da ita. Kuma har yanzu babu wanda ya san inda suka kai ta. “Wannan shi ne karo na farko da irin wannan abu ya faru da mu a wannan unguwa, ba a taba sace mutum ba sai a wannan karo,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ASP Numan Usman ya tabbatar wa wakilinmu aukuwar lamarin inda ya ce tuni suka soma gudanar da bincike don gano wadanda suka yi garkuwa da ita.
A halin da ake ciki kuma dan Majalisar Wakilai daga mazabar Akwanga da Wamba da Nasarawa-Eggon, Honorabul Dabid Umbugadu wanda abokin takarar wacce aka sace ne a zaben da ya gabata, ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa yana da hannu a cikin sace Mary Enwongulu. Ya fadi a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai cewa masu yada jita-jitar suna yi ne da nufin bata masa suna. Ya yi kira ga ’yan sanda su gaggauta bincike don gano tare da hukunta wadanda suka sace ta.
Ya ce “Kodayake na yi takara da ita kuma ta kai ni kotu inda take kalubalantar nasarata. Amma ba ni da wata matsala da ita don ’yar uwa ta ce.” Ya ce kafin ’yan bindigar su sace Mary Enwongulu sun yi fashi a wasu gidaje biyu da suke makwabtaka da ita a Akwanga, inda ya ce abin mamaki ne a ce yana da hannu cikin lamarin.
Fitaccen ‘yar siyasar dai majinta ya rasu sakamakon gajeriyar rashin lafiya, kwana biyu kafin a sace ta.