An sace yara 4 ’yan gida ɗaya a Kaduna
An yi garkuwa da ƙananan yara huɗu ’yan gida ɗaya a yayin da mahaifiyarsu ke jinya a asibiti a yankin New Millennium City a Jihar Kaduna
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace wasu ƙananan yara huɗu ’yan gida daya a yankin New Millennium City da ke Ƙaramar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
A cikin daren ranar Talata ne maharan suka kutsa gidan suka yi abin gaba da yaran — mata uku da ƙaninsu namiji, mai shekara biyu a duniya.
An sace yaran ne yayin mahaifunsu ya je asibiti domin dubiyar mahaifiyarsu, bayan an kwantar da tagwayen da ta haifa a kwanakin baya.
A kwanakin baya ne babbar cikin yaran mai shekara 15, ta yi saukar Karatun Al-Kur’ani. An sace ta ne tare da ƙanwarta mai shekara 12, da ’yar wan mahaifunsu, ’yar shekara tara.
Mahaifin yaran, Injiniya Yunusa Adamu, Sarkin Matsa, ya shaida wa Aminiya cewa, wani ƙanin yaran da ke barci ya tsallake rijiya da baya, maharan ba su gan shi ba.
Injiniya Yunusa, ya ce, “Da daddare abin ya faru, ka san tagwayen da matata ta haifa an kwantar da su a asibiti. Bayan mun baro wurinta a asibiti sai muka je muka sayi abinci na dawo gida.
“Amma da na shigo sai na samu gidan a buɗe, sun tafi da yaran. Ɗayan da ke barci ya lulluɓe jikinsa kuma ne kawai aka bari, ba su gan shi ba, Allah Ya kiyaye shi.”
Ya shaida wa wakilinmu cewa, “har yanzu babu wanda ya tuntuɓe mu a kan lamarin.”
Amma ya ce sun sanar da ’yan sanda da hukumar tsaro ta DSS game da faruwar lamarin.
Yankin New Millennium City da ke Kaduna yana yawan fama da ayyukan masu garkuwa da mutane.
Ko a watannin baya, Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bindiga suka kutsa unguwar Keke A a cikin dare suka yi awon gaba da kusan mutane 50, kafin daga bisani a sako su.