An sake bude cocin da ke ‘wajen da aka gicciye Annabi Isa’
Shugabannin coci a birnin Kudus sun sake bude cocin Holy Sepulchre kamar yadda rahotonni daga birnin kudus suka nuna. Sake bude cocin na zuwa ne bayan hukumomi a kasar Isra’ila sun dakatar da wani sabon tsarin haraji wanda ya yi sanadiyar rufe cocin a baya. BBC Ta ruwaito cewa shugabannin mabiya darikar Roman Catolika da […]

Shugabannin coci a birnin Kudus sun sake bude cocin Holy Sepulchre kamar yadda rahotonni daga birnin kudus suka nuna.
Sake bude cocin na zuwa ne bayan hukumomi a kasar Isra’ila sun dakatar da wani sabon tsarin haraji wanda ya yi sanadiyar rufe cocin a baya.
BBC Ta ruwaito cewa shugabannin mabiya darikar Roman Catolika da na Greek Orthodod da kuma na cocin Armenia sun soki tsarin ta hanyar rufe wani coci a wajen da kiristoci da dama su ka yadda cewa a nan ne aka gicciye Annabi Isa, a nan aka rufe shi kuma a nan aka tayar da shi zuwa sama.
Magajin garin Birnin Kudus Nir Barkat ya dakatar da sabon shirin harajin, kuma Firay Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kaddamar da kwamiti na musamman domin warware matsalar.