An tsawaita sassaucin dokar kulle da makonni hudu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake tsawaita sassaucin dokar kullen COVID-19 zango na biyu da makonni hudu. Karo na uku ke nan da ake sake jinkirta dage dokar da yanzu ake ciki a fadin kasa gaba daya. Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa don yaki da cutar, […]

An tsawaita sassaucin dokar kulle da makonni hudu

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, lokacin jawabin kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da coronavirus

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake tsawaita sassaucin dokar kullen COVID-19 zango na biyu da makonni hudu.

Karo na uku ke nan da ake sake jinkirta dage dokar da yanzu ake ciki a fadin kasa gaba daya.

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa don yaki da cutar, Boss Mustapha ya bayyana haka yayin jawabin kwamitin a Abuja ranar Alhamis.

A ranar Laraba kwamitin ya ziyarci Shugaba Buhari tare da yi masa jawabi kan inda aka kwana a kokarin da ake yi na yakar cutar.

Boss ya ce shawarar sake jinkirta dage kullen na daya daga shawarwarin da suka ba shugaban ya kuma amince da su.