An sake dawo da ‘yan Najeriya 153 daga Libya
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta sake karbar ‘yan Najeriya 153 wadanda aka dawo da su gida daga kasar Libya. Mista Slaku Lugard, ne ya wakilci Darakta Janar na Hukumar NEMA Mustapha Maihajja, lokacin karbar ‘yan Najeriyan da aka dawo da su yau Laraba a jihar Legas. ‘Yan Najeriyan sun sauka a […]
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta sake karbar ‘yan Najeriya 153 wadanda aka dawo da su gida daga kasar Libya.
Mista Slaku Lugard, ne ya wakilci Darakta Janar na Hukumar NEMA Mustapha Maihajja, lokacin karbar ‘yan Najeriyan da aka dawo da su yau Laraba a jihar Legas.
‘Yan Najeriyan sun sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas da misalin karfe 3:45 tsakar daren yau, a jirgi sama kirar Al Buraq Air Boeing 737.
A cikin wadanda aka dawo da su akwai ‘yan mata 59 da yara mata 4 da jarirai mata 7, sai kuma samari maza 78, yara maza uku da kuma jarirai biyu maza.