An sake gurfanar da shugaban majalisar dokokin jihar Legas a kotu

Hukumar yaki da cin hanci da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta sake gurfanar da shugaban majalisar dokokin Jihar Legas, Adeyemi Ikuforiji da mai taimaka masa na musamman Oyebode Alade Atoyebi, a ranar Litinin kan zargin aikata laifuka 54 na satar kudi.Sake gurfanar da su ya biyo bayan ritayar da alkalin kotun, Mai […]

An sake gurfanar da shugaban majalisar dokokin jihar Legas a kotu
An sake gurfanar da shugaban majalisar dokokin jihar Legas a kotu

Hukumar yaki da cin hanci da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta sake gurfanar da shugaban majalisar dokokin Jihar Legas, Adeyemi Ikuforiji da mai taimaka masa na musamman Oyebode Alade Atoyebi, a ranar Litinin kan zargin aikata laifuka 54 na satar kudi.
Sake gurfanar da su ya biyo bayan ritayar da alkalin kotun, Mai shari’a Okechukwu Okeke ya yi daga aiki, wanda shi ke yin shari’ar, amma a yanzu Mai shari’a Ibrahim Buba shi ya ci gaba da sauraron shari’ar.
Lauyan hukumar  EFCC, Cif  Godwin Obla  ya zargi shugaban majalisar dokokin jihar da mai taimaka masa na musamman da yin mu’amalar kudin da ta kai Maira miliyan 518 ta haramtacciyar hanya  tsakanin shekarar 2010 da shekarar 2011, wanda hakan ya saba wa dokar hana satar kudi. Amma Shugaban majalisar dokokin jihar da mai taimaka masa na musamman sun musanta zargin da ake yi musu.
Sai dai lauyoyin da ke kare shugaban majalisar da mai taimaka masa, Mista Tayo Oyetibo (SAN) da Tunde Akinrinmisi da kuma Abiodun Onidare sun fada wa kotun cewa suna yin taka-tsantsan wajen neman beli saboda tuni kotun ta ba da belin.
Alkalin kotun, Mai shari’a Buba ya umarci lauya Oyetibo ya shigar da bukatar neman belin wadanda ake zargi.
Daga nan sai Lauya Oyetibo ya ce ai tuni kotun ta bayar da belin shugaban majalisar inda babban jami’in gudanarwa na majlisar ya tsaya wa mutum na biyu da ake zargi.
Da yake mayar da martani lauya hukumar EFCC, Cif Obla ya ce shi ba ya jayayya da neman belin, amma abin da yake bukata shi ne a ci gaba da shari’ar ba tare da wani tsaiko ba.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Buba ya ba da belin su a kan Naira biliyan biyar tare da shaidun da za su tsaya musu da suka mallaki adadin kudin.
Alkalin ya ce dole su cika ka’idar belin cikin awanni 48, in ba haka ba kotun za ta ba da umarnin a kama su.
Daga bisani bayan lauyoyin wadanda ake zargi sun roki kotun ta rage yawan kudin belin, alkalin kotun ya rage zuwa Naira biliyan daya. Daga bisani ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa 25 ga watan Satumba.