An sake haihuwar ’yan hudu a Jihar Katsina
A ranar Talata da ta gabata ce, Allah Ya azurta Malam Zubairu, inda matarsa ta haifi ’ya’ya hudu a babban asibitin kwandala na karamar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina. Mahaifiyar yaran, wacce take zaune da mijinta a garin Gora da ke karamar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina ta samu haihuwar yaran ne, bayan da aka yi mata […]

A ranar Talata da ta gabata ce, Allah Ya azurta Malam Zubairu, inda matarsa ta haifi ’ya’ya hudu a babban asibitin kwandala na karamar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.
Mahaifiyar yaran, wacce take zaune da mijinta a garin Gora da ke karamar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina ta samu haihuwar yaran ne, bayan da aka yi mata aikin ciro su. Yaran hudu, maza uku da mace daya, suna cikin koshin lafiya, kamar yadda bayani ya tabbata daga hukumomin asibitin.
Wani matashin dan siyasa, Injiniya Muntari Sagir Malumfashi na daga cikin wadanda suka kai wa mai jegon da jariranta dauki. A lokacin da ya je dubiyar yaran, ya tallafa masu da kayan abinci da sutura. Haka kuma ya yi alkawarin ba su tallafin ragunan da za a yanka a ranar suna.
A makon da ya gabata ma, an samu wata mata a Jihar Sakkwato, wacce ta haifi ’yara hudu, maza uku da mace daya, wadanda aka rada wa suna Abubakar, Umar, Usman da kuma Fatima.
Ya zuwa rubuta labarin nan, mai jegon har yanzu tana kwance a asibitin ana kula da ita, duk da cewa yaran suna cikin koshin lafiya.