An sake kai hari wata Unguwa kusa da Maiduguri

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari Unguwar Mamannti wajen garin Maiduguri babban birnin jihar Borno . Maharan dai sun shiga garin ne akan Babura da misalin karfe 10:30 na dare inda suka fara budewa jama’ar garin wuta tare da kona gidajen jama’ar garin. Wasu ‘yan garin sun hijira sun […]

An sake kai hari wata Unguwa kusa da Maiduguri

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari Unguwar Mamannti wajen garin Maiduguri babban birnin jihar Borno .

Maharan dai sun shiga garin ne akan Babura da misalin karfe 10:30 na dare inda suka fara budewa jama’ar garin wuta tare da kona gidajen jama’ar garin. Wasu ‘yan garin sun hijira sun koma garin Molai  sanadiyyar harin.

A cewar rahoton, an kona gidajen jama’a da dama tare da kashe dabbobisu. A lokacin jama’ar garin suke ta kokarin barin garin, sai maharan suka ce, an gargade mu da kar mu kashe kowa a garin.