An sake kone ofishin ’yan sanda a Imo
Masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara sun matsa kaimi wajen kai hare-hare.
Wani ofishin ‘yan sanda da aka cinnawa wuta
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan awaren Biyafara ne na IPOB, sun kone wani ofishin ’yan sanda na yankin Atta da ke Karamar Hukumar Njaba a Jihar Imo.
Kazalika, ’yan ta da zaune tsayen sun kuma kone Kotun Majistire da wata Babbar Kotu a yankin na Atta tare da lalata wata cibiyar kiwon lafiya.
- Chelsea da City za su fatata a wasan karshe na Kofin Zakarun Turai
- An kashe mayakan Boko Haram 10 a garin Rann
Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne tsakanin karfe 1 na dare da kuma 2 na daren ranar Asabar.
Majiyar rahoton ta ce maharani sun kwashe tsawon sa’a biyu suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi kafin cinna wa gine-ginen wuta.
Sai dai yayin da aka tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, Bala Elkana, ya ce ba a sanar da shi game da faruwar lamarin ba.
A watannin baya bayan nan dai masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara sun matsa kaimi wajen kai hare-hare a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudancin Kasar.
A ranar Asabar ce ’yan awaren Biyafara suka sanya dokar hana fita wacce ta tilasta mazauna Jihar Imo kasancewa a gidajensu.