An sake kubutar da wani yaro da aka sace a Kano
A ci gaba da aikin kubutar da yaran da aka sace a Jihar Kano, Rundunar ’Yan sandan Jihar ta sake kubutar da wani yaro mai kimanin shekara 11 dan asalin jihar da aka sace shi tare da sayar da shi a garin Anacha da ke Jihar Anambra. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Haruna Abdullahi […]
A ci gaba da aikin kubutar da yaran da aka sace a Jihar Kano, Rundunar ’Yan sandan Jihar ta sake kubutar da wani yaro mai kimanin shekara 11 dan asalin jihar da aka sace shi tare da sayar da shi a garin Anacha da ke Jihar Anambra.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya shaida wa Aminiya cewa tun a shekarar 2014 aka sace yaron mai suna Ya’u a Unguwar PRP Bus stop a Karamar Hukumar Ungogo, inda aka tafi da shi zuwa Jihar Anambra.
DSP Haruna Abdullahi ya ce bincike ya nuna cewa shi ma wannan yaron kamar sauran yara tara da aka kubutar a kwanakin baya Mista Paul Onwe da matarsa Mercy Paul ne suka sace shi inda suka sayar da shi ga Madam Ebere Ogbodo a kan Naira dubu 200 suka kuma canja masa suna zuwa Chinedu Ogbodo.
A cewar Kakakin ’Yan sandan dukkan wadanda ake zargi suna hannu yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Ya kara da cewa rundunar tana yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta kubutar da sauran yaran da aka sace ko aka yi garkuwa da su.