An sake kwato dabbobi 174 daga barayi a Kaduna

Akalla sama da dabbobi 174 ne jami’an tsaro a Jihar Kaduna suka samu nasarar kwatowa daga hannun barayin shanu a karamar Hukumar Kajuru a jihar.Jami’an tsaron Operation Yaki na rundunar ’yan sandan jihar ne suka yi wannan nasara. Kakakin gwamnar jihar, Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya raba […]

An sake kwato dabbobi 174 daga barayi a Kaduna
An sake kwato dabbobi 174 daga barayi a Kaduna

Akalla sama da dabbobi 174 ne jami’an tsaro a Jihar Kaduna suka samu nasarar kwatowa daga hannun barayin shanu a karamar Hukumar Kajuru a jihar.
Jami’an tsaron Operation Yaki na rundunar ’yan sandan jihar ne suka yi wannan nasara. Kakakin gwamnar jihar, Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a makon jiya.
Ya ce jami’an tsaron sun samu bayanin sirri ne daga yankin, kafin suka garzaya zuwa dajin Lebere da ke Kajuru domin tunkarar barayin dabbobin.
Dabbobin da aka samu a dajin sun hada da shanu 145 da tumakai 20, sai jaki guda daya.
“barayin na ganin ’yan sandan sai suka rantaya a guje. Sai dai ana ci gaba da binchike domin kamo barayin shanun a yayin da kuma dabbobin aka kai su wajen ajiya domin raba wa masu su,” inji shi.
A wata sabuwa kuma, wasu da ake zargin ’yan kungiyar Sara-Suka ne su akalla 20 suka far wa wani matashi mai suna Muhammad Yusuf Abdullahi har suka ji masa rauni.
Da wani mai suna Abubakar Ibrahim na gida mai lamba  11 Kinshasha, daura da titin Shehu Laminu a Unguwan Rimi.
Bayanai daga yankin sun nuna cewa daukin da jam’an tsaro suka kai ne ya taimaka wajen maido da doka da oda. Su ma matasan da hango jami’an tsaro sai suka gudu amma su wadanda suka samu rauni tuni aka garzaya da su asibitin Barau Dikko, domin yi masu magani.