’Yan bindiga na farautar jami’an tsaro a Sabon Birni —Dan Majalisa

An sace mutum 17 kwana biyu bayan an yi wa jami’an tsaro kisan gilla a yankin.

’Yan bindiga na farautar jami’an tsaro a Sabon Birni —Dan Majalisa

‘yan bindiga

Dan Majalisa mai wakiltar Sabon Birni ta Gabas a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Sa’idu Ibrahim, ya ce yanzu ’yan bindiga suna neman jami’an tsaro a yankin.

Ya bayyana hakan ne bayan wani mahara sun sace sama da mutum 17 a garin Gawata da ke Karamar Hukumar kafin waywar garin Laraba.

Ya ce, “Suna neman sansanin jami’an tsaron ne tun bayan da suka samu karsashi bayan harin da suka kai garin Dama inda aka kashe sojoji da ’yan sanda da sibil defens.”

Dan majalisa ya bayyana cewa maharan suna kai farmakin ne a wuraren da sojoji da ’yan sanda da sauran jami’an suke zaune.

Ya kara da cewa sun kai hari a garin Gangara da Gatawa tun bayan da suka kashe jami’an tsaro.

Majiyar Aminiya ta ce daga cikin mutanen da aka sace a harin Gatawa har da wani mai suna Yahayan Tali.

“An je gidan Dogon Naira an tafi da iyalansa, haka sun tafi gidan kanen Hamza Ciwo, abubuwa marasa dadi sun faru a garin.

“An ce mana ana aiki amma barayin nan suna yin yadda suka ga dama, an dauke mana layin sadarwa ba mu gaisawa da kowa a waje ga barayi na yi mana yadda suke so, koyaushe matsalar nan karuwa take yi, kusan soja 20 aka yi wa sallah a satin da ya wuce; Bayan sun shiga garin Gangara suka yi wa garin kaca-kaca ba mu san wannan tsarin da ake nufi ba ta’addanci na karuwa.”

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50