An sake samun tsaiko a tattaunawar sulhu a Sudan ta Kudu

Yunkurin dawo da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu ya sake gamuwa da cikas, kwana biyu da fara tattaunawa tsakanin bangarori biyu da ba sa ga maciji. Masu shiga tsakani daga kungiyar kasashen gabashin Afirka (IGAD), a shekaranjiya Laraba sun bayyana cewa, bangaren ‘yan tawaye ya ki halartar zaman sasantawar a rana ta biyu, […]

An sake samun tsaiko a tattaunawar sulhu a Sudan ta Kudu
An sake samun tsaiko a tattaunawar sulhu a Sudan ta Kudu

Yunkurin dawo da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu ya sake gamuwa da cikas, kwana biyu da fara tattaunawa tsakanin bangarori biyu da ba sa ga maciji.
Masu shiga tsakani daga kungiyar kasashen gabashin Afirka (IGAD), a shekaranjiya Laraba sun bayyana cewa, bangaren ‘yan tawaye ya ki halartar zaman sasantawar a rana ta biyu, wadda ake yi a babban birnin kasar Ethiopia, Addis Ababa.
Har ila yau, kungiyar  IGAD ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba ga ‘yan tawayen domin su dawo teburin sulhu.
Ana ci gaba da fada a Sudan ta Kudu duk da kokarin da aka yi a baya na tabbatar da zaman lafiya.
A watan Disambar bara ne fada ya barke tsakanin dakarun da ke biyayya da Shugaban kasar Salba Kiir da wadanda ke goyon bayan mataimakinsa Riek Machar wanda hakan ya tilasta wa mutane fiye da miliyan daya kaurace wa muhallinsu.