An sake sassauta dokar hana fita a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sake sassauta dokar hana fita inda jama’a zasu iya zirgazirga daga karfe 6:00 na safe zuwa 5:00 na yamma. A wata sanarwa da mai taimaka wa Gwamnan Kaduna a harkar watsa labarai Samuel Aruwan ya fitar na cewa, jama’a zasu iya gudanar da harkokinsu daga lokutan da aka tsara. […]
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sake sassauta dokar hana fita inda jama’a zasu iya zirgazirga daga karfe 6:00 na safe zuwa 5:00 na yamma.
A wata sanarwa da mai taimaka wa Gwamnan Kaduna a harkar watsa labarai Samuel Aruwan ya fitar na cewa, jama’a zasu iya gudanar da harkokinsu daga lokutan da aka tsara.
Aruwan ya kara da cewa, Gwamnatin jihar ta dauki matakin ne bayan tattaunawar da kwamitin harkar tsaro ya yi da ayarin jami’an tsaron jihar.