An sake shirya wa Malamai jarabawar gwaji a Kaduna
Gwamnatin jihar ta ce ta sake yin gwajin ne don inganta harkar ilimi a jihar.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake shirya wa malaman firamare da ke Jihar, jarabawar gwaji don tabbatar da kwarewarsa a fannin koyarwa.
Wannan shi ne karo na biyu, cikin shekara hudu da ake shirya wa malaman makamanciyar wannan jarbawar.
- Babban Hafsan Tsaron Indiya, matarsa da sojoji 11 sun mutu a hatsarin jirgi
- Jirgi ya yi hatsari da Babban Hafsan Tsaron Indiya
A baya dai, an kori wasu malamai 22,000 daga cikin wadanda suka fadi jarabawar, sannan aka dauki sabbi guda 25,000, wanda gwamnatin ta ce sun cancanta.
Yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, Shugaban Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar, Tijjani Abdullahi, ya ce ba don a kori malamai aka shirya jarabawar ba.
“An shirya jarrabawar ne don gano wuraren da ake da bukatar yin gyara da kuma bai wa malaman horo.
“Malaman da suka zauna wannan jarrabawar za su ga sauyi kan yadda za a gudanar da ita,” inji shi.
A shekarar 2017 ne Ma’aikatar Ilimin Jihar ta sallami malaman makaranta fiye da 20,000, wanda a cewarta ba su cancanci ci gaba da koyarwa a Jihar ba.