An sake tsare matar liman bisa kashe dan kishiyarta

Rundunar ’yan sanda da ke kula da garin Samaru ta sake kama amaryar Liman da ake zargi da kashe dan kishiyarta mai suna Musiliha, wadda take Layin Makabarta, Hayin Dogo, Samaru Zariya. DPO Mannir Lawal ya ce duk da ba a ba su damar magana da ’yan jarida ba amma ya ce sun janye belin […]

An sake tsare matar liman bisa kashe dan kishiyarta
An sake tsare matar liman bisa kashe dan kishiyarta

Rundunar ’yan sanda da ke kula da garin Samaru ta sake kama amaryar Liman da ake zargi da kashe dan kishiyarta mai suna Musiliha, wadda take Layin Makabarta, Hayin Dogo, Samaru Zariya.

DPO Mannir Lawal ya ce duk da ba a ba su damar magana da ’yan jarida ba amma ya ce sun janye belin da suka ba Musiliha, tun da ta haihu lafiya kuma sun karbi sakamakon da asibiti ta bayar. Ya ce za su tura su babban ofishinsu da ke Kaduna, domin ci gaba da bincike.
Idan ba a manta ba, rundunar ’yan sandan ta shaida wa Aminiya cewa, ta ba da belinta a baya ne, a bisa shawarar jami’an kiwon lafiya, ganin tana dauke da tsohon ciki kuma ta fara nuna alamun haihuwa.
A nata bangaren, wacce aka kashe dan nata, Hauwa’u Ahmed, ci gaba da bayyana abin da ke damunta ta yi, a sakamakon kashe dan nata mai suna Ahmed Umar Liman, dan kimanin shekaru tara da haihuwa da kuma bibiyarta da kishiyarta ke yi na neman halaka. Ta ce a sakamakon bin hakkinta a kan lamarin, mijin nata ya yi mata saki uku.
“Mijina Malam Umar Liman ya yi mini wannan saki ne a kan na ce ban yarda ba sai an fitar mini da hakkin dana Ahmed da kishiyata ta halaka shi da duka. Tun ba yau ba, mijina Liman ya kasa daukar matakin kare mu daga ukubar da amaryata Musiliha ke ba mu, da ni da ’ya’yana. Na farko, ta taba juye mini talge a kafafuwana, sai da na kusan wata biyu ina jinya. Na biyu, ta taba yi wa Ahmed marigayi dukan kawo wuka tare da furucin cewa sai ta kashe shi, nan ma ya kasa daukar mataki; wanda har sai da na kai kara gaban mai unguwa aka kasa sulhuntawa. Sai da muka je wurin ’yan sanda, amma duk da haka sai da ta aikata abin da ta furta a kan dana, ta kashe Ahmed. Don na ce ban yarda ba shi ne ya yi mini saki uku amma wannan sakin ba zai dame ni ba har sai na bi hakkin dana,” inji Hauwa’u.