An sake yin garkuwa da Farfesa a Adamawa

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Farfesa Allan Kadams daga tsangayar tsirrai a jami’ar fasaha ta Modibbo Adama (MAUTECH) Yola a jihar Adamawa. An dai yi garkuwa da Kadams ne mako biyu da yin garkuwa da Farfesa Ibrahim Adamu dake Jami’ar wanda aka saki kwana daya kafin a sake yin garkuwan da wani Farfesan. Rijistarar […]

An sake yin garkuwa da Farfesa a Adamawa

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Farfesa Allan Kadams daga tsangayar tsirrai a jami’ar fasaha ta Modibbo Adama (MAUTECH) Yola a jihar Adamawa.

An dai yi garkuwa da Kadams ne mako biyu da yin garkuwa da Farfesa Ibrahim Adamu dake Jami’ar wanda aka saki kwana daya kafin a sake yin garkuwan da wani Farfesan.

Rijistarar jami’ar Hajiya Halima Bala ta tabbatar da yin garkuwa da Farfesan a yau Talata.

An yi garkuwa da Farfesan ne a masaukinsa dake rukunin gidaje na Bajabure a wajen garin Yola.