An sake zaɓen Obasa Kakakin Majalisar Legas
Mojisola Meranda ta yi murabus daga muƙamin ne bayan shafe kwanaki 49 tana mulki.

Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus.
Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda.
- Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki
- HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja
Bayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya.
’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa.
Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar game da yadda za a shawo kan rikicin.
Mojisola Meranda dai ta yi murabus daga muƙamin ne bayan shafe kwanaki 49 tana mulki.
Meranda ta hau kujerar kakakin majalisar ne bayan da ’yan majalisar suka tsige Mudashiru Obasa a ranar 13 ga watan Janairu.
Meranda, wacce ta jagoranci zamanta na ƙarshe a yau Litinin, ta sha yabo da jinjina.