An sake zabar Balarabe Abdullahi a matsayin Shugaban Majalisar Jihar Nasarawa
Wakilan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun sake zabar Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi a matsayin Shugaban Majalisar Jihar a karo na biyu. Alhaji Balarabe Abdullah na Jam’iyyar APC yana wakiltar Mazabar Udage da Umaisha a Karamar Hukumar Toto. ’Yan majalisar ne baki daya suka zabe shi ba tare da ya fafata da wani dan takara ba […]
Wakilan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun sake zabar Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi a matsayin Shugaban Majalisar Jihar a karo na biyu. Alhaji Balarabe Abdullah na Jam’iyyar APC yana wakiltar Mazabar Udage da Umaisha a Karamar Hukumar Toto. ’Yan majalisar ne baki daya suka zabe shi ba tare da ya fafata da wani dan takara ba a zaman farko na majalisar da suka yi a Lafiya, kuma nan take Akawun Majalisar Mista Ego Maikeffi Abashi ya rantsar da shi.
A jawabin godiya Alhaji Balarabe Abdullahi ya gode wa abokan aikinsa dangane da sake zabarsa, inda ya ce, “Ina tabbatar muku na amince da zabena da kuka yi kuma da yardar Allah ba zan ba ku kunya ba. Na dauki alkawari zan ci gaba da gudanar da shugabanci nagari da girmama juna da tsoron Allah da tafiya da kowa kamar yadda muka yi a baya don samun nasarar majalisar da jiharmu baki daya.”
Dan Majalisa mai wakiltar Mazabar Nasarawa-Eggon ta Arewa, Mohammed Muluku ya ce ’yan majalisar baki daya sun yanke shawarar sake zabar Alhaji Balarabe Abdullahi ne bayan sun yi la’akari da kyawawan shugabancinsa da ya ce ya kawo ci gaba da dama a majalisar da jihar baki daya a shekara 4 da suka gabata, inda ya bukace shi ya ci gaba da hakan.