An ceto ƙananan yara 4 da aka yi garkuwa da su a Kaduna
Ƙananan yaran nan guda huɗu ’yan gida ɗaya da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su sun kuɓuta.
Ƙananan yaran nan guda huɗu ’yan gida ɗaya da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna, sun kuɓuta.
A daren ranar Litinin ɗin nan aka damƙa yaran su huɗu ga iyayensu baya Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro, ya taimaka wajen ceto su daga hannun masu garkuwa da su.
- Gobara ta yi ajalin jami’in Kwastam da Iyalansa 5 a Osun
- Majalisar dokokin Kano ta yi watsi da dokar gyaran haraji
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya raka iyayen yaran zuwa Abuja, inda aka damƙa musu ’ya’yan nasu mata uku da namiji ɗaya bayan an ceto su.
Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Tsaro, Nuhu Ribadu, ya mika yaran, waɗanda ɗaya daga cikinsu marainiya ce.
Yaran masu shekaru biyu da tara da 12 da kuma 14 an sace su ne a gidansu a daren ranar Talata da ta gabata.
An yi awon gaba da su ne, yayin da mahaifunsu ya je dubiyar mahaifiyarsu da ke jinyar ƙannensu tagwaye a asibiti.