Almajirai 15 da aka sace a Sakkwato sun shaƙi iskar ’yanci

Ɗaliban sun shaki iskar ’yanci bayan shafe makonni biyu a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

Almajirai 15 da aka sace a Sakkwato sun shaƙi iskar ’yanci

Ɗalibai 15 da aka sace a wata makarantar allo da ke Jihar Sakkwato sun shaki iskar ‘yanci.

Dan Majalisar Dokoki ta Jihar Sakkwato mai wakiltar mazabar Gada ta Gabas, Honorabul Haruna Dauda ya ce an ceto yaran ne bisa ga kokarin mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Sakkwato.

Ya ce kwamandan sojojin Najeriya da ke Sakkwato ne ya miƙa yaran da wasu mata da aka ceto su goma sha takwas.

A cewarsa, Gwamnan Sakkwato, Ahmad Aliyu, ya umurci a duba lafiyar mutanen da aka ceto.

Daga bisani bayan tabbatar da ƙoshin lafiyarsu an miƙa mutanen ga Shugaban Karamar Hukumar Gada da sauran shugabannin yankin domin a sadar da su da iyalansu.

Aminiya ta ruwaito cewa, makonni biyu da suka gabata ne aka sace ɗaliban a ƙauyen Gidan Bakuso da ke Karamar Hukumar Gada a Jihar Sakkwato.

Ana iya tuna cewa, Liman Abubakar wanda shi ne malamin makarantar allon da aka sace almajiran, ya ce ’yan bindigar sun shigo cikin tsakiyar gari sun kamo wata mata sai suka biyo ta wajen makarantarsa, inda almajiransa suka ji kukan wannan mata da suka kamo.

Ya ce ɗaliban nasa suna da yawa sai suka tashi su ka yi ta shiga cikin dakunansu yayin da ‘yan bingar suka tisa keyar wasu da dama daga cikin almajiran.

Daga bisani dai ’yan bindigar da suka sace almajiran sun buƙaci a biya su kuɗin fansa har naira miliyan 20 kafin su sako su.

Alaramman Tsangayar, Liman Abubakar ne ya bayyana haka ga wakilinmu a ranar Talatar makon jiya

Ya ce, “’yan bindigar sun kira ni sau biyu yau da safe.

“A waya ta farko, sun tambaye ni ko ban damu da halin da ɗalibaina suke ciki ba shi ya sa ban tuntube su ba?

“Sai na ce musu ba ni da lambarsu shi ya sa. Sai su ka ce, in jira za su sake kira da misalin ƙarfe 11 na safe.

“Bayan karfe 11 na safe, sai suka sake kira, suka umarce ni da in je in zauna da Hakiminmu, in faɗa masa cewa ya nemo Naira miliyan 20, domin su sake su.

“Na roke su amma sun ce ba za su rage komai ba. Na je na tattauna batun da hakimin ƙauyenma amma har yanzu ba mu cimma matsaya ba.