An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Sakin nasu na zuwa ne, bayan sakin wasu sojojin Isra’ila mata da hamas ta yi, wadanda ke rike a hannunta tsawon watanni.

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Isra’ila ta sako Falasɗinawa 200 daga cikin waɗanda take riƙe da su a kurkuku kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas ta tanada.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Hamas ta saki rukuni na biyu na ’yan Isra’ilar da ta yi garkuwa da su — wasu sojojin Isra’ila mata da Hamas take riƙe da su tsawon watanni.

A wata sanarwa da hukumomin gidan yari na Isra’ila suka fitar sun ce: “Bayan kammala dukkanin abubuwan da suka wajaba a gidajen yarin da kuma amincewar hukumomi an saki dukkanin ’yan ta’addan daga gidajen yari na Ofer da Ktziot,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP da na Reuters suka ce.

Sai dai sabanin Falasɗinawan da aka saki a makon da ya gabata waɗanda yawanci hukuncinsu na zaman gidan yari kaɗan ne, a wannan karon, 121 daga cikin fursunonin suna kan hukuncin rai da rai ne — wasu bisa laifin kisan kai fiye da sau daya da ya hada da kisan farar hula ’yan Isra’ila.

Shekarun Falasɗinawa fursunonin sun bambanta sosai, inda mafi ƙanƙanta da aka saki shi ne mai shekara 16, yayin da mai shekara 69 ya kasance mafi girma a cikinsu.

Ɗaya daga cikin fursunonin ya shafe shekara 39 a gidan kurkukun Isra’ila, bayan da aka kama shi da farko a 1986.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin manyan laifuka mafiya tsanani ba sa cikin waɗanda aka saki yau.

Kusan 70 daga cikinsu za a fitar da su daga Isra’ila ne inda za a bi da su ta Masar zuwa ƙasashe makwabta da suka haɗa da Qatar da Turkiyya, kafin a kai su Falasɗinu.