An saki Faston da aka kama kan kashe yarinya

An ba da belin Fasto Ofuche Ukoha limamin cocin Perfect Christianity Mission da ke unguwar Surulere a jihar Legas wanda ake zargi da umartar yaro dan shekaru 18 mai suna Ikechukwu Friday ya kashe budurwa mai suna Bose Ogoja ya kawo masa kashinta.Wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta ba tabbatar wa  Aminiya […]

An saki Faston da aka kama kan kashe yarinya

An ba da belin Fasto Ofuche Ukoha limamin cocin Perfect Christianity Mission da ke unguwar Surulere a jihar Legas wanda ake zargi da umartar yaro dan shekaru 18 mai suna Ikechukwu Friday ya kashe budurwa mai suna Bose Ogoja ya kawo masa kashinta.
Wata majiya da ba ta so a bayyana sunanta ba tabbatar wa  Aminiya cewa an ba da belin Fasto Ukoha tun a karashen makon da ya gabata.
Amma sai dai mai magana da yawun rundunar yansanda a Jihar Legas, Ngozi Braide ta ce ba ta da labarin sakin nasa amma za ta bincika don gano gaskiyar lamarin.
Ngozi ta bayyana cewa da zarar sun kammala bincike za su gurfanar Faston a gaban kuliya.
Majiyar ta ce an ba da belinsa Faston ne ba tare da wani sharadi ba sakamakon umarnin da suka samu daga manya.
Yaron mai suna Ikechukwu ya kashe Bose ’yar kimanin shekaru 12 da haihuwa ta hanyar shake ta a wani gini da ba a kammala ba yayin da ya je shagonsu sayan abinci amma nan take asirinsa ya tonu aka mika shi ga ’yan sanda.
Friday ya fada wa ’yan sanda cewa Fasto Ukoha ne ya umarce shi ya kashe yarinyar  ya kawo masa kashinta bisa alkawarin zai biya shi ladan naira dubu dari, amma shi Fasto Ukoha ya musanta zargin da yaron ya yi.
Fasto Ukoha ya shaida wa ’yan sanda cewa bai taba ganin yaron ba, sharri ne aka kulla masa don a bata masa suna.
Sai dai ana cikin haka ne mahaifiyar yaron mai suna Esa Egbo ta bayyana wa manema labarai cewa danta karya ya yi wa Fasto Ukoha kuma aljani ne ke sanya shi yake kashe ’yan mata tare da yunkurin yi musu fyade.
Esa Egbon ta ce sau hudu ’yan sandan da ke unguwar Badagiri suna kama danta kan zargin yunkurin yi wa kananan yara da shekarunsu ya kama daga 10 zuwa 15 fyade.
Ta ce ita da iyalanta membobin cocin Perfect Christianity Mission ne da ke unguwar Surulere inda Fasto Ukoha yake shugabanta, amma danta bai taba yin alaka da faston ba kamar yadda ya yi zargi.
Ta bayyana cewa, danta ya fara nuna wadansu dabi’u munana ne tun lokacin da wani makwabcinsu ya tsine masa a kan ya daki ’yarsa.
“Tun lokacin ya fara nuna wadansu munanan dabi’u, kuma ya taba gaya mini cewa wani aljani ya shiga jikinsa a kan hanyarsa ta zuwa makaranta. Saboda yunkurin yi wa ’yan mata fyade har sai da ta kai muna raka shi makartanta ni da mahaifinsa. Lokacin da ya rubuta jarabawarsa ta NECO sai da muka rika raka shi. Kuma ni da mahaifinsa muke zuwa muna bai wa iyayen yaran da ya yi yunkurin yi musu fyade hakuri. Sakamakon haka ya bar gida. Yunkurin fyade na karshe da ya yi shi ne a ranar 10 ga watan Disemban shekarar 2013  inda aka kama shi aka gurfanar da shi a kotu aka yanke masa hukuncin zaman gidan kaso, sai da na samu lauya sannan aka fito da shi. Ita wannan yarinyar ya gaya min cewa ya je zai ci abinci a inda suke sayar da abinci yana zaune sai yarinyar ta zo wucewa sai ya ji wani abu ya shiga jikinsa, sai kawai ya tashi ya bi ta ya rungume ta kamkam, sai kawai ta mutu. Duk cikin yarana shi ne yaro mai natsuwa wanda ba ya son tashin hankali’. In ji ta.