An saki magoya bayan Arsenal da suka yi murnar lallasa United
An amince a sake su kowa ya kama gabansa amma an gindaya musu sharuda.
An saki magoya bayan Arsenal da aka kama kan murnar nasarar da kungiyar ta a samu a wasan hammaya tsakaninta da Manchester United.
BBC ya ruwaito an cafke magoya bayan takwas a garin Jinja na Uganda, lokacin da suke murnar nasarar da kungiyarsu ta samu a wasan hamayya da United a gasar Firimiyar Ingila.
- Har yanzu ban taba ganin sabbin takardun Naira ba —Gwamna Ortom
- Dan takarar Gwamnan Abiya na PDP ya rasu
Lokacin da aka kama su a ranar Litinin, suna sanye da rigunan Arsenal da kuma wani kofi a hannunsu.
’Yan sanda sun kama magoya bayan – wadanda ke cikin jerin gwanon motoci ranar Litinin da safe – inda daya daga cikinsu ke rike da kofin da suka hada kudi suka saya a wani shago a kasar.
’Yan sanda sun ce babu wanda ya ba su umarnin yin wannan murna wadda za ta iya haifar da rikici a cikin al’umma.
Kakakin ’yan sanda na yankin James Mubi, ya ce bayan wata tattaunawa da aka yi tsakanin jami’an tsaro, an amince a sake su kowa ya kama gabansa amma an gindaya musu sharuda.
Daya daga cikin magoya bayan ya fada wa ’yan jarida cewa “sun nemi umarni gabanin wannan murna da suka gudanar da nasara kan Man United”.
Arsenal dai ta samu nasara a kan abokiyar hamayyarta Manchester United da ci 3-2 a wasan na ranar lahadi.
Sakamakon ya bai wa kungiyar tazarar maki biyar a saman teburin Firimiyar Ingila, lamarin da ya bai wa magoya bayanta a fadin duniya kwarin gwiwar daukar kofin karon farko cikin shekara 19.