An saki sabon bidiyon ‘Yan Matan Chibok
Gidan talabijin na CNN ya yada wani sabon faifan bidiyo wanda a cikinsa aka ga wadansu ‘yan mata guda 15 daga cikin ‘Yan Makarantar garin Chibok fiye da 200 da Kungiyar Boko Haram suka sace yau tsawon shekaru biyu ke nan. Kafar yaɗa labaran ta ce a watan Disamba ne ta samu faifan bidiyon daga […]

Gidan talabijin na CNN ya yada wani sabon faifan bidiyo wanda a cikinsa aka ga wadansu ‘yan mata guda 15 daga cikin ‘Yan Makarantar garin Chibok fiye da 200 da Kungiyar Boko Haram suka sace yau tsawon shekaru biyu ke nan.
Kafar yaɗa labaran ta ce a watan Disamba ne ta samu faifan bidiyon daga hannun wani wanda yake kokarin ganin an sasanta tsakanin ‘yan kungiyar Boko Haram da gwamnatin Najeriya don sakin ‘yan matan.
A cikin faifan bidiyon dai, ana ganin ‘yan mata guda 15 sanye da bakaken hijabi, kuma suna jingine da wani gini mai launin ruwan dorawa.