An saki Sarkin da ya miƙa kansa kan zargin kisan sojoji 17 a Delta
Rundunar Sojin ta ce har babu wanda ta wanke game da zargin kisan dakaru 17 a Delta.
Hukumomin sojin Najeriya sun saki Sarkin da aka ayyana nemansa ruwa a jallo bisa zargin hannu kisan dakarun soji 17 a Okuama da ke Ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce duk da cewa rundunar ba ta wanke kowa ba game da zargin, amma ta yanke shawarar sakin sarkin ne bayan shiga tsakani da wasu mutane masu kima a cikin al’umma suka yi da kuma nazari mai zurfi.
- Kisan Sojoji: Basaraken da ake nema ya miƙa kansa ga ’yan sanda
- Ana neman mutane 8 ruwa a jallo kan kisan sojoji a Delta
Aminiya ta ruwaito yadda rundunar soji ta ƙaddamar da farautar waɗanda ake zargi da aikata munanan aika-aikar da ta sa mazauna garin Okuama suka fice daga cikin unguwannin garin.
Jim kaɗan bayan samamen da jami’an suka kai, sojoji sun bayyana sunayen: Arthur Ekpekpo, farfesa; Andaowei Dennis Bakriri, Akevwru Daniel Omotegbono (wanda aka fi sani da Amagbem); da Akata Malawa David, waɗanda ake nema ruwa a jallo.
Sauran mutanen da aka bayyana sunayensu sun haɗa da: Sinclear Oliki, da Clement Ikolo Ogenerukevwe da Reuben Baru, da Igoli Ebi, mace ɗaya tilo a cikin waɗanda ake nema ruwa a jallo.
Bayan sanarwar sojojin, Sarkin wanda lamarin ya faru a yankinsa mai suna Clement Ikolo Ogenerukevw ya miƙa kansa ga ‘yan sanda, inda su kuma suka miƙa shi ga sojoji.
Yayin da yake miƙa shi ga Sanata mai wakiltar Delta ta tsakiya a hedikwatar rundunar a ranar Juma’a, Nwachukwu ya ce Sanatan ya shaida halin kirki na sarkin.