An sako Alkalin babbar kotun Ondo da aka yi garkuwa

An sako Alkalin babbar kotun jihar Ondo Mai shari’a Abdul Dogo, wanda aka yi garkuwa da shi kwana biyar da suka wuce. An dai sako Abdul ne da misalin karfe 2 na tsakar daren ranar Asabar. Rahoton bai bayyana an biya kudin fansa ko kuma ba a biya ba. Masu garkuwa da mutane sun sace […]

An sako Alkalin babbar kotun Ondo da aka yi garkuwa

An sako Alkalin babbar kotun jihar Ondo Mai shari’a Abdul Dogo, wanda aka yi garkuwa da shi kwana biyar da suka wuce.

An dai sako Abdul ne da misalin karfe 2 na tsakar daren ranar Asabar.

Rahoton bai bayyana an biya kudin fansa ko kuma ba a biya ba.

Masu garkuwa da mutane sun sace alkalin ne a garin Ibilo da ke iyakar jihar Ondo da jihar Edo a ranar Talata.