An sako Basaraken Abuja bayan biyan kudin fansa Naira Miliyan 6.5

An sako Sarkin Rubuchi HRH Mohammed Ibrahim Pada, da ke Karamar Hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja. Masu garkuwan da mutanen sun sako Basaraken ne bayan an biya su kudin fansa Naira Miliyan 6.5. An dai yi garkuwa da Mohammed Ibrahim, da safiyar ranar Larabar da ta wuce. Bayan ‘yan bindigar sun  shiga garin […]

An sako Basaraken Abuja bayan biyan kudin fansa Naira Miliyan 6.5

An sako Sarkin Rubuchi HRH Mohammed Ibrahim Pada, da ke Karamar Hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja.

Masu garkuwan da mutanen sun sako Basaraken ne bayan an biya su kudin fansa Naira Miliyan 6.5.

An dai yi garkuwa da Mohammed Ibrahim, da safiyar ranar Larabar da ta wuce. Bayan ‘yan bindigar sun  shiga garin na Rubuchi.

Wani da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, a yanzu haka Basaraken yana cikin koshin lafiya bayan kwana hudu a hannun masu garkuwan.