An sako dalibai mata 78 da aka sace a Kamaru
A ranar Larabar da ta gabata ce aka sako daliban da aka sace daga wata makarantar kwana a yankin Kudu maso Yammacin Kamaru. An sace daliban, su 78 da wasu mutum uku ne a ranar Lahadi a birnin Bamenda. An kuma sako wani direba, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a sako shugaban […]
A ranar Larabar da ta gabata ce aka sako daliban da aka sace daga wata makarantar kwana a yankin Kudu maso Yammacin Kamaru. An sace daliban, su 78 da wasu mutum uku ne a ranar Lahadi a birnin Bamenda.
An kuma sako wani direba, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a sako shugaban makarantar da wani malami ba. Cocin Presbyterian na Kamaru ya ce an yashe yaran ne a wani gini da ke garin Bafut, wanda ke da nisan kilomita 24 daga birnin Bamenda.
Jami’i Mai Kula da Harkokin Cocin Presbyterian na Makarantar, Rabaran Fonki Samuel ya ce “Yan bindigan da suka sace su sun sako su cikin sauki da kwanciyar hankali. Daga nan sai aka kawo su zuwa harabar cocinmu.”
“Bayanan farko da muka samu daga wadanda suka sace daliban shi ne sun kira mu ta wayar tarho suna cewa suna son sako yaran a ranar Talata da safe, amma saboda wani ruwa mai karfi da aka tafka a ranar, shi ya hana a sako sun. Amma da yammacin Talatar, kuma cikin ikon Ubangiji, sai kawai a ka dawo mana da yaran,” inji shi.
Cocin Presbyterian din kuma ya bayyana cewa satar daliban na Lahadi shi ne karo na biyu da aka sace yaran makarantar a kasa da mako guda. A ranar 31 ga watan Oktoba, an sace wasu daliban makarantar 11, amma aka sake su. Ba a san ko suwa ne ne suka sace yaran ba.
Gwamnati da ‘yan aware a yankin mai amfani da harshen Ingilishi sun rika nuna wa juna yatsa, inda suke dora laifin sace daliban akan junansu. Ministan sadarwar kasar, Issa bakary Tchiroma ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “an sako dukkan dalibai 79” amma bai yi karin haske kan batun ba.