An sako dalibai uku da aka yi garkuwa da su a Kaduna

An sako dalibai uku da ’yan bindigar Birnin Gwari suka sace a watan Maris 2020 bayan sun dawo daga rubuta jarabawar shiga Jami’a. An sace daliban ne tare da wata ’yar karamar kanwarsu a kusa da wani guri da ake kira Unguwar Yako da ke hanyar karamar hukumar Birnin Gwari zuwa Kaduna. A cewar majiyar […]

An sako dalibai uku da aka yi garkuwa da su a Kaduna

An sako dalibai uku da ’yan bindigar Birnin Gwari suka sace a watan Maris 2020 bayan sun dawo daga rubuta jarabawar shiga Jami’a.

An sace daliban ne tare da wata ’yar karamar kanwarsu a kusa da wani guri da ake kira Unguwar Yako da ke hanyar karamar hukumar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

A cewar majiyar mu da ke Birnin Gwari, an sako daliban ne uku kusan kwanaki 10 da suka wuce bayan an biya kudin fansa.

Aminiya ta ruwaito labarin sace yaran a cikin watan jiya da yadda ’yan ta’addan suka kashe direban motar da daliban ke ciki mai suna Ibrahim Dawo.