An sako jagoran ’yan adawan Habasha

Mahukuntan kasar Habasha sun sako jagoran ’yan adawan kasar, Mista Merera Gudina bayan ya shafe sama da shekara daya a tsare a kurkuku.  Jami’an kurkuku sun shaida wa iyalansa cewa an sako shi a shekaranjiya Laraba da safe inda aka bar shi ya koma gidansa. Mista Gudina yana tsare ne a kurkuku tun watan Disamban […]

An sako jagoran ’yan adawan Habasha

Mahukuntan kasar Habasha sun sako jagoran ’yan adawan kasar, Mista Merera Gudina bayan ya shafe sama da shekara daya a tsare a kurkuku. 

Jami’an kurkuku sun shaida wa iyalansa cewa an sako shi a shekaranjiya Laraba da safe inda aka bar shi ya koma gidansa.

Mista Gudina yana tsare ne a kurkuku tun watan Disamban shekarar 2016, inda ake zarginsa da aikata ayyuka da dama ciki har da alaka da kungiyoyin ’yan ta’adda.

Gwamnatin Habasha ta fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa za ta janye tuhume-tuhumen da take ga sama da mutum 500 da ake zargi da aikata ba daidai ba.

A farkon wannan wata ne gwamnatin ta ce za ta yi afuwa tare da janye wasu shari’u da aka yi wa ’yan siyasa da dama da wadanda shari’unsu suke gaban kotuna a wani yunkuri na karfafa hadin kan kasa. 

Sanawar ta biyo bayan sama da shekara biyu ana gudanar da bore don nuna adawa da gwamnati, inda masu zanga-zanga suka rika kiraye-kiraye a sake fasalin harkokin siyasa da na tattalin arziki tare da kako karshen almundahana a tsakanin jami’an gwamnatin da kuma daina cin zarafin dan Adam.

Gwamnatin Habasha dai ta sha musanta cewa akwai fursunonin siyasa a kasar, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin jama’a da ’yan adawa suke zargi.