An sako soja da iyalansa da aka yi garkuwa da su a Taraba
An sako jami’in soja da iyalansa da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ranar Asabar a hanyar karamar hukumar Wukari zuwa karamar hukumar Ibbi a jihar Taraba. Majiyarmu ta gano cewa, an sako jami’in sojan ne da iyalansa a jiya Lahadi da daddare. Rahotanni na bayyana cewa, sojoji da ‘yan sanda sun kai […]
Masu garkuwa da mutane
An sako jami’in soja da iyalansa da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ranar Asabar a hanyar karamar hukumar Wukari zuwa karamar hukumar Ibbi a jihar Taraba.
Majiyarmu ta gano cewa, an sako jami’in sojan ne da iyalansa a jiya Lahadi da daddare.
Rahotanni na bayyana cewa, sojoji da ‘yan sanda sun kai samame kauyen Ibiwa inda aka yi garkuwa da jam’in sojan. Jami’an tsaron sun baiwa jama’ar garin umarnin awa 24 akan sako sojan da iyalansa.