An sako limamin Katolika da aka sace a Kaduna

Amos, wanda ke aiki a Cocin St. Gerald Ƙuasi Parish ya dawo gida lafiya lau ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare, kwana ɗaya bayan sace shi.

An sako limamin Katolika da aka sace a Kaduna

An sako limamin cocin Katolika, Rabaran Fada Ibrahim Amos wanda ’yan bindiga suka sace a ranar Alhamis da rana a Kurmin Risga da ke Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna.

Fada Amos, wanda ke aiki a Cocin St. Gerald Ƙuasi Parish ya dawo gida lafiya lau ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare, kwana ɗaya bayan sace shi.

Bayani kan sakin nasa na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Cocin Diocese na Kafanchan, Rabaran Fada, Dakta Jacob Shanet ya fitar, inda ya gode wa Allah tare da nuna godiya ga al’umma bisa addu’o’i da goyon baya da suka bayar a lokacin da lamarin ya faru.

Fada Shanet ya jinjina wa ƙoƙarin ƙungiyoyin tsaro na gari, ’yan sanda da jami’an DSS da suka ba da gudunmawa a lokacin da aka sace limamin.

Yankin Kudancin Kaduna na daga cikin wuraren da rikice-rikice da garkuwa da mutane suka yawaita.