An sako ma’aikacin asibitin da aka sace bayan biyan fansa a Kaduna
Masu garkuwa da mutane da suka sace wani ma’aikacin asibiti mai Suna Abdulrashid Lawal a gidansa da ke a Tudun Barde a Rigasa Kaduna sun sake shi bayan ya biya kudin fansa. Masu Garkuwan sun sake shi ne da misalin karfe 12: na rana bayan an biya Naira dubu dari 350. Sai dai Aminiya ta […]
Masu garkuwa da mutane da suka sace wani ma’aikacin asibiti mai Suna Abdulrashid Lawal a gidansa da ke a Tudun Barde a Rigasa Kaduna sun sake shi bayan ya biya kudin fansa.
Masu Garkuwan sun sake shi ne da misalin karfe 12: na rana bayan an biya Naira dubu dari 350.
Sai dai Aminiya ta samu labarin cewa Yusuf Ishak Rigasa wanda shi ne ya kai masu kudin famsar shima bai dawo ba sai da suka yi garkuwa da shi kuma suka amshi kudin fansa akansa.
“Eh an sake shi a ranar Litinin din nan da ta wuce bayan sun karbi Naira dubu dari 350 wanda ni aka bai wa kudin in kai masu a wani guri da ake kira Doguwa a cikin daji.
“Bayan na kai masu kudin ne sai daya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya make ni. Ni ban san inda kaina yake ba sai dai kawai bude ido na yi na ganni a xaure kuma ido na a rufe da kyelle. Haka na zauna da su har tsawon kwanaki hudu. Kuma sai da aka kara masu Naira dubu xari 3 wannan yasa suka kyalemu muka dawo. Yanzu dai mun biyasu Naira dubu dari 650 ne a matsayin kudin famsa mu biyu,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa ya wahala matuka a hannun masu garkuwa da mutanen kafin daga bisani suka kyalesu domin a cewarsa hatta abinci ma idonsu a rufe yake haka kuma zuwa bayan gida.