An sako ma’aikatan gonar Obasanjo da aka yi garkuwa da su
Babu wanda aka kama kan alaka da garkuwa da manyan jami’an.
Ma’aikatan da aka yi garkuwa da su a gonar tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, sun shaki iskar ’yanci bayan ’yan bindigar sun sako su.
’Yan bindigar sun bude wa motar gonar Obasanjo wuta, suka yi awon gaba da Babban Jami’in Kudi da Mai Binciken Kudade da Babban Manajan Ajiya na kamfanin Obasanjo Holdings zuwa cikin jeji.
Lamarin na ranar Labara ya faru ne lokacin da manyan jami’an kamfanin na Obasanjo Holdings ke tafiya a cikin motar a kan babbar hanyar Kobape zuwa Abeokuta, a daidai a kauyen Seseri da ke kusa da garin Kobape na Karamar Hukumar Obafemi-Owode ta Jihar Ogun.
A ranar Juma’a Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya sanar da cewa masu garkuwar sun sako ma’aikatan gaba dayansu ba tare da an biya kudin fansa ba.
Ya ce an sako ma’aikatan kamfanin na Obasanjo ne bayan matsin lambar da jami’an rundunar suka yi wa masu garkuwa da mutanen.
Ya ce, “Tabbas tun jiya (Alhamis) muka hana masu garkuwar sakat domin runduwar SWAT da ta yaki da masu satar mutane na ta bin sawunsu a daji.
“Sun kuma gano mutanen da aka yi garkuwa da su a cikin daji a kusa da kwalejin Day Waterman; Tun jiya suke can.
“Yau (Juma’a) kuma aka sako su ba tare da wani lahani ba ko biyan kudin fansa.”
Sai dai ya ce har zuwa lokacin babu wanda aka tsare kan alaka da garkuwa da ma’aikatan da aka yi, “Amma muna da kwarin gwiwa cewa akwai wanda za mu kama.”