An sako Malam Isa Gausu bayan wata 22 a tsare

Jami’an Tsaron kasa (SSS) da ke Abuja sun sako fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma shugaban Salafiyya da ke Bidda Malam Isah Muhammad Awwal wanda aka fi sani da Malam Isah Gausu da kanensa Malam Muhammad Ahmad Liman.Mutanen biyu sun koma gidansu da ke birnin Bidda, bayan tsare su da aka yi tun cikin watan […]

An sako Malam Isa Gausu bayan wata 22 a tsare

Jami’an Tsaron kasa (SSS) da ke Abuja sun sako fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma shugaban Salafiyya da ke Bidda Malam Isah Muhammad Awwal wanda aka fi sani da Malam Isah Gausu da kanensa Malam Muhammad Ahmad Liman.
Mutanen biyu sun koma gidansu da ke birnin Bidda, bayan tsare su da aka yi tun cikin watan Yunin shekarar 2012.
Malam Isah Muhammad Awwal ya iso garin Bidda ne a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 4:30 na rana inda magoya bayansa maza da mata manya da yara suka yi ta tururuwa zuwa gidansa domin yi masa barka da arziki.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce jami’an tsaron suka kira shi daga inda yake tsare domin ya rattaba hannu a wadansu takardun da aka bukaci ya cike.
Wasu lauyoyi masu zaman kansu da suka shiga cikin lamarin da iyalin malamin da wasu daga cikin almajiransa da ’yan uwa da abokan arziki suka nemi yadda za a samu mafita game da lamarin don ya dawo cikin iyalinsa, ya kuma ci gaba da gudanar da harkokinsa na da’awa yadda ya saba.
Malam Isah Muhammad Awwal yayin da ya yi wa dimbin magoya bayansa jawabi, ya danganta lamarin da cewa kaddara ce daga Allah, Wanda Yakan jarrabi bayinsa ta hanyoyi daban-daban musamman wadanda suka rungumi koyar da addinin Musulunci kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya aiwatar a rayuwarsa.
Malamin wanda ya nuna zaman kason da ya yi na kusan shekara biyu da cewa yana tare da darussa masu yawa ya nanata cewa zai ci gaba da gudanar da al’amuransa na koyar da darussan da ya saba, tare da da’awa ga almajiransa.Ya ce manyan bayin Allah da suka bi irin wannan hanyar sun fuskanci kalubale masu yawa ba tare da gwiwarsu ta yi sanyi ba.
A karshe, ya yi godiya ga dukkan muatnen da suka taimaka masa da addu’o’i daga farko zuwa karshen wannan jarrabawa da kuma wadanda suka taimaka wa mahaifiyarsa da iyalinsa ta hanyoyi da dama wadanda ya dawo ya same su cikin koshin lafiya, baya ga mahaifiyarsa da take fama da lalurar hawan jini.
Malam Umar Ndagi wanda aka fi sani da Nma Bala wanda kawun malamin ne, ya shaida wa Aminiya cewa, bayan murna da sako malamin da suka yi, sun gode ga Madaukakin Sarki wanda Ya ba su baki daya da mahaifiyarsa juriya da hakurin halin da suka samu kansu. Sai dai ya ce babban darsin da suka dauka bayan da Gausu ya share lokaci mai tsawo ba ya tare da su, shi ne yadda al’amura suka yi ta gudana gwargwadon hali.
Malam Nasiru Ahmad daya daga cikin almajiran malamin, ya shaida wa wakilinmu cewa sun rasa jagora a lokacin da malaminsu ba ya tare da su, domin al’amarin karatu da da’awa sun nemi tsayawa cik. Sai dai manyan dalibansa suka rika koyar da akasarin wadanda suke can baya.