An sako malamai biyu da a ka kama bayan tashin bam a Madalla

Malamai biyu da aka kama a garin Madalla ta Jihar Neja, Malam Muhammad Adam Madalla da Malam Muhammad Sani sun koma cikin iyalansu a makon jiya, bayan sun shafe shekara biyu a tsare. Malam Muhammad Adam dai malami ne da ke koyarwa kuma limami a daya daga cikin masallatan Juma’a na garin, yayin da shi […]

An sako malamai biyu da a ka kama bayan tashin bam a Madalla
An sako malamai biyu da a ka kama bayan tashin bam a Madalla

Malamai biyu da aka kama a garin Madalla ta Jihar Neja, Malam Muhammad Adam Madalla da Malam Muhammad Sani sun koma cikin iyalansu a makon jiya, bayan sun shafe shekara biyu a tsare. Malam Muhammad Adam dai malami ne da ke koyarwa kuma limami a daya daga cikin masallatan Juma’a na garin, yayin da shi kuma Malam Muhammad Sani shugaba ne na wata makaranta mai suna Millatu Ibrahim a garin Madalla. Aminiya ta samu labarin cewa mutanen biyu na tsare ne a hannun jami’an tsaron ’yan sandan ciki (DSS) da ke Minna ta Jihar Neja, tun makon farko da tashin bam a cocin wani Katolika a Madalla a karshen shekarar 2011. An sako ne daidai da daidai a ranar Litinin da kuma Juma’a ta makon jiya. An sako su ne bayan da Hakimin Madalla Malam Musa Z. Sa’idu ya sa hannu a madadin iyalansu kamar yadda Hakimin ya tabbatar wa wakilinmu. Haka kuma an sako wani mai sana’ar dinki da rini mai suna Malam Ibrahim dan Zariya wanda dan asalin garin Zariya ne mazaunin garin, inda ya samu tabin hankali a yayin zamansa a hannun jami’an tsaron. A ganawarsa da wakilinmu Malam Muhammad Adam Madalla, wanda ya ce ya je wa’azin kasa na kungiyar Izala a Jigawa a ranar da bam din ya tashi, amma aka kama shi kwana biyar bayan aukuwar lamarin a gidansa da ke garin Madalla. Ya bayyana lamarin a matsayin wata jarrabawa, kuma ya ce ya bar komai ga Allah. Ya yi  fatar jami’an tsaron za su hanzarta sako daya daga cikin wadanda aka tsare daga garin kan matsalar, mai suna Alhaji Sani Muhammad wanda ya ce direba ne da ke sufuri tsakanin Abuja da Kano.