An sako malaman kwalejin da aka yi garkuwa da su a Makarfi

An sako malaman Kwalejin Kiwon Lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi a Jihar Kaduna awa 24 bayan yin garkuwa da su lokacin da aka sace su a hanyarsu ta komawa Makarfi daga Zariya a ranar Litinin da ta gabata. Kantoman Kwalejin, Malam Yusuf Yakubu Arrigasiyu ya tabbatar da sakin malaman ta hanyar sakon waya […]

An sako malaman kwalejin da aka yi garkuwa da su a Makarfi
An sako malaman kwalejin da aka yi garkuwa da su a Makarfi

An sako malaman Kwalejin Kiwon Lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi a Jihar Kaduna awa 24 bayan yin garkuwa da su lokacin da aka sace su a hanyarsu ta komawa Makarfi daga Zariya a ranar Litinin da ta gabata.

Kantoman Kwalejin, Malam Yusuf Yakubu Arrigasiyu ya tabbatar da sakin malaman ta hanyar sakon waya da ya tura wa wakilinmu. “Ina sanar da ku cewa malamaina uku da aka yi garkuwa da su a ranar Litinin, an sako su da misalin karfe takwas na dare ranar Talata kuma ni Kantoman Kwalejin ne na tattauna da wadanda suka yi garkuwa da malaman kuma suka yarda suka ba ni malaman muka dawo tare,” inji shi.

Malaman da aka yi garkuwa da su kuwa sun hada da Daraktan sashin kula da hakora, Mista Elisha Damina Akawu da Rabi’at Malami Dogo da Halima Rilwan, dukkansu malamai ne a bangaran hakora a kwalejin.

Kamar yadda bayanai suka iske Aminiya, malaman suna kan hanyarsu ta dawowa daga Zariya zuwa Makarfi ne, suka fada hannun masu garkuwa da mutane, bayan sun halarci jarabawa da hukumar kula da lafiyar hakora ta kasa ta yi musu a otel din Teejay da ke Zariya.

Tun da farko, a safiyar Talata, an ga motar da suke tafiya da ita an yar a tsakanin Tashar Yari zuwa kwalejin, an fasa tayar motar guda daya.

Sai dai wata majiya da ba ta so a ambaci sunanta ba ta shaida wa Aminiya cewa an samu malaman ne a wani kauye da ke kusa da wani gari mai suna Nasarawan Doya, a Karamar Hukumar Makarfi da ke Jihar Kaduna kuma ya ce an biya kudin fansa kafin a sako su, amma bai san ko nawa ba ne.