An sako matan Shugaban Karamar Hukumar da aka sace a Jigawa

Maharan sun yi awon gaba da matan biyu ne a daren Juma’ar da ta gabata.

An sako matan Shugaban Karamar Hukumar da aka sace a Jigawa

Wadanda suka sace matan Shugaban Karamar Hukumar Kiyawa da ke Jihar Jigawa, Nasiru Ahmad, su biyu, sun sake su.

An sace matan ne a Karamar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi a karshen makon da ya gabata.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ne ya tabbatar da sako matan biyu da maraicen Talata.

Ya ce bayan sakin nasu, an garzaya da su babban asibitin Dutse domin duba lafiyarsu.

Sai dai bai yi karin haske a kan ko an biya kudin fansa ba kafin a saki matan.

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne wasu ’yan bindiga suka kutsa kai gidan Ciyaman din, sannan suka yi awon gaba da matan.

Maharan sun shiga garin ne da dare inda suka dinga harbi babu kakkautawa, kafin daga bisani suka shiga gidan kai-tsaye suka tafi da matan.

Matar aure ta banka wa mijinta wuta

Abin da ya sa na yi wa Buhari juyin mulki —IBB

Yadda aka kama ɗan shekara 65 ɗauke da bindiga

Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan mangwaro a makaranta