An sako matar da aka kama saboda bayar da aron waya
Matar nan da sojoji suka kama saboda ba da aron waya a Suleja da ke Jihar Naje Malama Fatima Ahmad ta komo gidan mijinta a ranar Talatar da ta gabata.Idan za a iya tunawa a ranar Asabar 3 ga Mayu ne sojojin suka kama ta bayan ta ara wa wata makwabciyarta waya, ta kira mijinta, […]
Matar nan da sojoji suka kama saboda ba da aron waya a Suleja da ke Jihar Naje Malama Fatima Ahmad ta komo gidan mijinta a ranar Talatar da ta gabata.
Idan za a iya tunawa a ranar Asabar 3 ga Mayu ne sojojin suka kama ta bayan ta ara wa wata makwabciyarta waya, ta kira mijinta, lamarin da ya jawo mata share kwana 40 a hanun jami’an tsaro na farin kaya a Abuja.
Da ta ke zantawa da wakilinmu a shekaranjiya Laraba, Fatima Ahmad, ta ce jami’an tsaron su ka kula da ita da danta na goye a tsawon lokacin da take tsare.
Ta ce kamar yadda suka shaida mata kamata ya biyo bayan ba da aron wayar da ta yi ne ga makwabciyarta da ba su dade da kama haya a gidan da take aure a Unguwar Magaji a garin Suleja ba. Ta ce matar wadda mijinta ya ce shi likita ne da ke aiki a Jihar Taraba, tashe-tashen hankula ya sa shi yin hijira zuwa Suleja, kuma ta amshi lambar wayarta ta ba mijin a yayin da zai yi tafiya kwana hudu da kama daki a gidansu.
“Kuma a ranar ne mijinta ya kira wayar kafin Sallar Magariba inda na ba ta wayar ta yi magana da shi. Bayan kamar kwana uku ya sa ke bugo wayar da dare suka yi magana, inda ta sanar da ni cewa mijinta zai turo wani ya dauke ta zuwa inda yake kafin kwana biyu, saboda ya samu aiki a wani wuri da gidan zama. Sai dai na bayyana mamakina a kan al’amarin rashin zuwa da kansa sai dai ya turo wani.”
Ta kara da cewa “A daren ne sojoji suka kutso gidan suka kama matar, daga baya suka dawo suka kama ni bayan sun nemi wayar ta sanar da su cewa tawa ce ta ara,” inji ta.
Ta ce bayan sojojin sun kama ta a daren sun je garin Kwankwashe a kusa da Suleja suka kama buduruwar mijinta wadda ita ma suka ce ya kira ta ta waya a daren. Ta ce bayan sojojin sun kai su Abuja sun mika su ga jami’an tsaro na farin kaya, daga bisani suka kai matar mutumin da ke da tsohon ciki zuwa wani asibiti inda ake kula da ita.
Fatima ta ce an sako budurruwar mijinta a ranar Litinin, ita kuma aka sako ta a ranar Talata bayan an kira mijin ta waya don dauko zuwa gida.
Mijin matar Malam Ahmadu Ibrahim ya nuna godiyarsa ga Allah a kan fitowar matarsa tare da dansu ya kuma nuna farin ciki kan yadda jami’an tsaron suka kula da su.