An sako mutanen da aka sace a rukunin gidaje a Abuja

Wadanda aka sako sun hada da wasu kananan yara biyu da wata uwa da ’ya’yanta uku da kuma ma’aikaciar otel

An sako mutanen da aka sace a rukunin gidaje a Abuja

’Yan bindiga sun sako mutane bakwai da ke hannunsu cikin mutum 10 da suka sace a Rukunin Gidajen Sagwari da ke unguwar Dutsen Alhaji da ke Abuja.

Aminiya ta gano cewa a daren Asabar ne masu gurkuwa da mutanen suka sako su bayan an biya kudin fansa.

Kimamanin makonni uku ke nan da mahara suka kutsa rukunin gidajen, suka sace mutane 10 a ranar Lahadi.

Daga bisani ranar Juma’a suka kashe uku daga cikinsu, ciki har da wata dalibar Jami’ar Bayero ta Kano, mai suna Talatu Salihu.

Sauran biyun su hada da wata ’yar sakandare mai shekaru 13 Mitchell Ariyo da wani ma’aikacin otel da ke unguwar, mai suna Akpagher Joseph Terzungwe.

Bayan kashe su ne masu garkuwar suka kara kudin fansan da suke nema kan kowane mutum zuwa Naira miliyan 100, tare da barazanar kashe su idan ba a kawo kudin zuwa ranar Laraba  ba.

Wata majiya da ke rukunin gidajen ta shaida wa wakilinmu a safiyar Lahadi cewa mutane bakwan da aka sako sun hada da wasu kananan yara biyu da wata uwa da ’ya’yanta uku da kuma ma’aikaciar otel da ke makwabtaka da rukunin gidajen.

Majiyar ta kara da cewa tuni iyalan wadanda aka sacen suka sauya wurin zama zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa